Palliative Portal

GWAMNATIN KANO ZATA GUDANAR DA BINCIKE KAN MUTANEN DA AKA KASHE A LOKUTAN ZABE.


Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wasu hukumomi da za su binciki yadda gwamnatin da ta gabata ta yi tasarrufi da kudade da kadarorin gwamanti da kuma bin ba’asin mutanen da aka kashe a lokutan zabe.

Da yake kaddamar da hukumomin guda biyu a gidan gwamnati, gwamna Abba Kabir Yusuf ya alkawarta cewa gwamnati zata dauki matakin doka kan duk wanda aka samu da laifi.

Ya ce, hukumomin zasu binciki ba’asin mutanen da suka bata a sakamakon rigingimun siyasa a lokutan zabe tun daga shekarar 2015 zuwa 2023.

Gwamna Abba Kabir ya kuma kara da cewa gwamnati ba zata kyale kisan da aka yiwa al’umma a shekarar 2023 ya tafi ba tare da an dauki matakan Sharia ba.

Ya ce hukumar zata binciki rigingimun siyasa da kuma bibiyar ba’asin mutanen da aka kashe daga shekarar 2015 -2023, inda zata kasance karkashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf.

Ya kara da cewa, hukuma ta Biyu zata binciki yadda gwamnatin da ta gabata ta yi tasarrufi da kudade da kadarorin gwamnati zata karkashin jagorancin mai Sharia Farouk Lawan.

Yayi kira ga hukumomin Biyu da su gudanar da ayyukansu bisa gaskiya da rikon amana tare da tabbatar da cewa an yiwa alumar jihar Kano adalci.

ADVERT

Advertise your product and services easily on Nigeria’s first online grains market.

Click here Open Mart to get started or visit Openmart.ng

Did you know you could get 1 GB data plan with less than N300 only.

Visit www.data4metopup.ng or simply download the app HERE

FOR MORE NEWS AND UPDATESPLEASE JOIN OUR WHATSAPP GROUP

CLICK HERE TO JOIN PALLIATIVE PORTAL WHATSAPP GROUP 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button