Campus PortalHausa Portal

JAMI’AR AHMADU BELLO ZATA SAMAR DA KARIN DAKUNAN KWANAN DALIBAI

Jami’ar Ahmadu Bello ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya don samar da dakunan kwanan dalibai masu gadaje 1600 a Jami’ar karkashin tsarin hadin gwiwar.

Jami’ar da kamfanin raya kasa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ne suka sanya hannu a yarjejeniyar.

Mataimakin shugaban jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabiru Bala, da magatakardar Jami’ar, Malam Rabi’u Samaila, ne suka sanya hannu a madadin jami’ar, yayin da shugaban sashen samar da zuba jari na kamfanin, Dipo Lawore, ya rattaba hannu a madadin kamfaninsa.

Da yake jawabi a wajen taron, mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Kabiru Bala, ya bayyana jin dadinsa kan ci gaban da aka samu, ya kuma bada tabbacin cewa aikin zai taimaka matuka gaya wajen dakile babban gibin da ake samu wajen samar da wurin kwana mai kyau ga daliban makarantar.

Tun da farko a jawabinsa dangane da aikin, shugaban sashen hulda da kamfanoni masu zaman kansu na jami’ar, Dakta Mu’awiya Abubakar, ya bayyana cewa Asusun Tallafawa Manyan Makarantu na Kasa wato TETFUND ce ta dauki nauyin gudanar da aikin.

ADVERT

Advertise your product and services easily on Nigeria’s first online grains market.

Click Here to get started or visit Openmart.ng

Did you know you could get 1 GB data plan with less than N300 only.

Visit www.data4metopup.ng or simply download the app HERE

FOR MORE NEWS AND UPDATESPLEASE JOIN OUR WHATSAPP GROUP

CLICK HERE TO JOIN PALLIATIVE PORTAL WHATSAPP GROUP 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button