Hausa Portal

MAJALISAR DOKOKIN JIHAR KANO TA JA KUNNEN KAMFANIN RARRABA WUTA NA KEDCO

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jiha da ta dakatar da kamfanin rarraba wutar lantarki na KEDCO daga yanke wuta a na’urorin rarraba wutar lantarki 170 (Transformer) dake cikin kananun hukumomin Kiru da Bebeji da Karaye da Rogo da sauran kananan hukumomi dake makwabtaka da su.

Da yake gabatar da kudirin, Dan majalissar jiha mai wakiltar karamar hukumar Kiru, Alh. Usman Abubakar Tasi’u ya ce ya samu rahoton cire wuta a yankunan alhali al’umar yankunan ne suke sayen na’urorin rarraba wutar tare da biyan kudin gyaran su ba kamfanin KEDCO ba.

Ya ce bisa tanadin doka sai an baiwa abokin hulda sanarwar yanke wuta aƙalla na tsawon makonni Biyu kafin yanke wuta.

Zaman majalisar wanda shugaban majalisar Alh. Jibril Ismail Falgore ya jagoranta ya bukaci gwamnatin jihar Kano ta binciki ayyukan kamfanin rarraba wuta na KEDCO wanda mafi yawan al’umma ba su gamsu da shi ba tare da tabbatar da ganin abokan huldarsa suna gamsuwa da aiyukansa a Kano.

Radio Kano


ADVERT

Advertise your product and services easily on Nigeria’s first online grains market.

Click here Open Mart to get started or visit Openmart.ng

Did you know you could get 1 GB data plan with less than N300 only.

Visit www.data4metopup.ng or simply download the app HERE

FOR MORE NEWS AND UPDATESPLEASE JOIN OUR WHATSAPP GROUP

CLICK HERE TO JOIN PALLIATIVE PORTAL WHATSAPP GROUP 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button